Ephesians 2

1Amma da ku matattu ne cikin zunubanku da laifofinku. 2A cikinsu kuka yi rayuwa bisa ga al’amuran duniyan nan. Kuka biye wa mai sarautar ikokin sararin sama, wannan ruhun ne da ke aiki cikin kangararrun ‘ya’ya. 3Da can dukanmu muna cikin wadannan marasa bada gaskiya. Muka biye wa mugun burin jikinmu. Muna aikata halin mutuntaka da na tunaninmu. Bisa ga dabi’a ‘ya’ya ne wadanda sun cancanci fushin Allah, kamar wadansu.

4Amma Allah mai yalwar jinkai ne, sabili da matukar kauna da ya kaunace mu. 5Sa’anda muke matattu cikin zunubai, ya kawo mu cikin sabon rai tare da Almasihu. Ta wurin alheri aka cece mu. 6Allah ya tashe mu tare ya kuma sa muka zauna tare a matsayi guda cikin Almasihu Yesu. 7Ya yi wannan domin a zamanai masu zuwa ya nuna mana matukar yalwar arzikin alherinsa ta wurin Yesu. Yana nuna mana wannan ta wurin alherinsa.

8Domin ta wurin alheri aka cece ku ta wurin bangaskiya, wannan ba daga gare ku ba ne, kyauta ce ta Allah. 9Ba daga ayyuka ba, Saboda wannan dalili kada kowa ya yi fahariya. 10Gama mu aikin hannuwansa ne, halitattu cikin Almasihu Yesu domin mu yi kyawawan ayyuka, wadanda tun da Allah ya tanada, mu yi rayuwa a cikinsu.

11Saboda haka ku tuna da ku al’ummai ne a dabi’ar jiki. Ana kiranku “marasa kaciya”, abin da ake kira kaciya cikin jiki wadda hannayen mutane ke yi. 12Gama a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu. Ku bare ne ga mutanen Isra’ila. Ku baki ne ga wa’adodi na al’kawarai. Ba ku da tabbaci a kan gobe. Ba ku da Allah a cikin duniya.

13Amma yanzu a cikin Almasihu Yesu ku da da kuke nesa da Allah, an kawo ku kusa da shi ta wurin jinin Almasihu. 14Gama shine salamar mu. Domin ya mai da biyun daya. Cikin jikinsa ne ya rushe katangar gaba da ta raba mu da juna. 15Wato ya kawar da shari’a mai umarnai da sharudda, domin ya halitta sabon mutum daya a cikinsa. Yin haka ya kawo salama. 16Ya yi haka domin ya sulhunta mutum biyu cikin jiki daya ga Allah ta wurin gicciye. Ta wurin gicciye ya kashe gabar da ke tsakaninsu.

17Yesu ya zo ya yi maku shelar salama ku da kuke nesa da ku na kusa. 18Domin ta wurin Yesu dukanmu biyu cikin Ruhu daya muna da hanya zuwa wurin Uba.

19Sabo da haka yanzu ku al’ummai, ko daya, ba bare ba ne. Maimakon haka ku abokai ne tare da kebabbun Allah, abokan aiki. 20Wadanda an gina su bisa tushen manzanni da annabawa. Almasihu Yesu da kansa shine mafificin dutsen ginin. 21A cikinsa dukan ginin ya hade tare, suna kuma girma kamar haikali cikin Ubangiji. A cikinsa ne kuma ake gina ku gaba daya kun zama mazaunin Allah a cikin Ruhu.

22

Copyright information for HauULB